Daren Yalda na daya daga cikin tsofaffin bukukuwan Iran, dare ne mafi tsawo da duhu na shekara, mutanen Iran sukan shirya yin liyafar cin abinci mai daɗi da kuma 'ya'yan itatuwa iri-iri, galiban kankana da rumman. Bayan an gama cin abincin sai a karanta kundin wakoki na Shahnameh da sauran kissoshi